Pinned onto Entertainment
– Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari yayi sabon naɗi a ofishin kasafin kuɗi
– Buhari ya naɗa Akabueze a matsayin Darekta-Janar
– Naɗin zai canza fuskar Ma’aiktar shirye-shirye da kasafin kuɗi
Femi Adesina, wanda shine ke ba Shugaban Kasa shawara a kan harkar watsa labarai ya sanar da cewa Shugaban kasar ya amince na naɗin mai ba shawara a kan harkar kasafin kuɗin kasa a matsayin sabon Darekta-Janar na ofishin kasafin kuɗi da shirye-shiyen kasa. Akabueze zai canji Mista Tijjani Mohammed wanda shi yanzu zai yi aiki a matsayin mai ba Shugaban kasa shawara kan harkokin shirye-shirye, inda zai yi aiki tare da Ministan kasafin kuɗi da shirye-shirye.
KU KARANTA: Yan Boko Haram sun kai ahri a cikin jihar Yobe
Akabueze da Tijjanin sun fara aiki da ma’aikatar kasafin ne a watan Fubrairun shekarar nan. Wannan sauyi da aka yi, yana cikin yunkurin da ake yi wajen tabbatar da cewa ma’aikatar ta tafiyar da tsare-tsaren ta kamar yadda ya dace. Inji Femi Adesinan.
Akabueze yayi aiki a matsayin Manajan Darakta na Bankin NAL PLC a shekarar 2000. Ya kuma rike babban Daraktan zartarwa na Bankin Sterling a shekara ta 2006. Mista Akabueze yayi aiki a ma’aikatu kamar su Gidan Talibijin na Kasa watau NTA, da kuma Pricewaterhouse. Da ma kuma Bankuna kamar su; Citibank, Fedelity da kuma Bankin Afrika na UBA.
Ya rike kwamishinan tattali da kasafin kuɗi na jihar Legas daga shekarar 2007 zuwa 2015. Har ila yau yana rike da matsayin Darakta a kamfanin ‘Chams’ daga watan Febrairun Shekarar na. ya kuma rike matsayin Daraktan a bankin Sterling har zuwa Agustan 2006.
Ya karbi kyauttuka na JF Kennedy, Kyautar sukolashif daga Gwamnatin Tarayya tun daga shekarar 1980 zuwa 1982, Shine wanda ya zo na biyu a jarabawar ilmin akanta a shekarar 1984, da ma dai sauran su.
Mista Akabueze mamba ne na ICAN, wata kungiya ta kwararrun akantoci, haka zalika mamba ne na FCA. Kuma dai mamban girmamawa ne na CIBN. Mista Akabueze bai tsaya a nan ba, ma’aikacin banki ne, akanta, kuma babban jami’in gudanarwa, ga shi masanin tattalin arziki. Yana da digiri mai makin farko watau ‘Faskila’ a ilmin akanta daga Jami’ar Legas da ke Najeriya. Kuma tsohon dan makarantar nan ta Legas ne na kwarewa a harkar kasuwanci.
The post Buhari ya nada sabon Darekta–Janar na Ofishin kasafin kudi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.
from fornaija.com http://ift.tt/1PN4hE1
via fornaija
No comments:
Post a Comment